Wace Ce Ita (Who Is She) Complete Hausa Novel Written By Barakancy

Wace Ce Ita Complete Hausa Novel Written By Barakancy


Posted byAiHausa Novel
PriceFree
CategoryHausa Ebooks
Uploaded On26 Jan, 2023
Upload Time8:29 pm
Hits218 Views
Author

Barakancy

Writer Group

Nil

Novel Genre

CommentNo Comments

Wace Ce ita Complete Hausa Novel Written By Barakancy

     A hankali ta bude fuskarta data kudindine a cikin hijab, ko bata duba agogo ba tasan karfe hudun asuba ne saboda lokacin ta saba tashi,kuma tinda ta sabarwa kanta tashi karfe hudun farilla,bata taba fashi ba……. Kallon hagu da dama tayi ta sauke wani gajeran ajiyar zuciya,ko baa fadamata ba tasan duk bacci suke…..


     Mikewa tayi tsap still fuskarta a cikin hijab din,a hankali take takawa har ta isa bakin locker dinta,budewa tayi ta dauki bucket da sponge case dinta ta fita……


    A hankali ta shigo dakin still fuskarta a cikin hijab din,shiri ta soma a gaggauce saboda wanka da alwala ya jata kusan 40mins,gashi tanaso tayi nafilfili kafin a tada sallah,ita dama haka take komanta a sanyayye takeyi,shiyasa har mamakin yanda takeda fada akeyi,duk da dama ita ba magana ta tabayi da yan room din ba amma a reaction dinta zaka gane masifaffiya ce


      Shiryawa tayi cikin blue black abaya,ta saka socks da handgloves, tasa hijab,ta saka niqab saman hijab din sannan ta tada sallah……. Bayan ta idar da laziminta ta kalli bangon dakin taga kusan shida saura,tabe baki tayi ta kalli yan room din one by one tana sakar musu harara,dama haka suke in ba tashinsu tayi ba sai sukai takwas kafin wata ta motsa,har mamaki suke bata,gwarama Eesha taji suna cemata kowa?… Oho dai!……


   Ninke sallaya tayi tabi gadajensu duka ta daka musu duka. Eesha ce kawai ta bude ido,kallonta tayi tace “ke wlh mutum na tashi daga bacci yawani ganki da niqab,wlh harna tsorata”…… Dauke Kai kawai tayi dan badan darajar sallah ba ko kallo bata ishe taba….. Eesha ko dama tasan ba kulata zatayi sai ta mike tana cewa “Ai kindai samu lada da kika tashemu musamu muyi sallah,yan wahalan nan ma kila saina zuba musu ruwa zasu tashi”…. Ko kallonta bata karayi ba tacigaba da harkar gabanta….


    Cornflakes ta hada ta shiga gyaran bed dinta sannan ta shige,daman room of 4 ne kuma bed din double bunk ne,ita kuma a kasa take…. Bayan tashige tayi unfolding wani coverage da tayiwa bed din yanda bame hangota,ta soma shan cornflakes dinta…


Eesha ko tama kasa mikewa daga kan bed dinta tsabar binta da kallo da tayi,itadai kullum a ranta sai tace “Allah kadai yasani kodai da aljana muke zaune,dama ance suma ana karatu dasu,ace kullum mutum boye kanshi,muna room daya amma bamu san ya kike ba,muga kafar ma da hannun ina duk kinbi kin rufe,gashi ba mgn ba kula kowa?…. Hmmm shiyasa nake binki a hankali inma aljana ce kyamin da sauki”……


Tana gama sha ta fito ta kuma gyara bed din tsap,dama ba itace da shara ba kasancewar roller coaster sukeyi,sanda sukayi making roll dinma kasa tinkarta sukayi,haka dai suke daure suka mata mgn,bata ce musu komai ba kuma dama basuyi expecting zata ce ba,amma ga mamakinsu yana zuwa kanta sai suka ga tayi,shikenan indai yazo Kanta tun asuba ma takeyi hartasa tirare,ta kuma sakeyi da yamma….. Inko ta dawo taga dakin kacha kacha tsintsiya kawai zata dauko ta mikawa duk wanda taga dama,jiki na rawa meshi zeyi,shikenan kowa yakeyi da huri,dako wani sai ya kai yamma beyi kona safe ba…… Saida tagama kimtsa komai sannan ta fice daga dakin…….. 


     A hankali take takawa harta isa lecture hall din,wani spot ta samu a front sit ta zauna,haka kawai ranar taji tana sha’awar zaman gaba dan duk yanda take fitowa da wuri dan yawanci ma itake fara shiga class din amma bata zaman gaba sai baya…. Tana zama idonta ya sauka akan wall clock din class din taga 20mins after 7,rasama me zatayi kafin 8 tayi a fara lectures tayi,karatu kuma will be the last abu da zatayi,dan ita gani take bazata iya zama wani karatu ba shiyasa kawai take zuwa class tazo ta gane abinda zata iya ganewa,ba ruwanta da wani maimaici,shiyasa ko notebook bata taba siya ba bare tayi wani jotting,shi kanshi handouts din ma bata taba siyaba,exam dinma in yazo ba karatu take ba,in taci shikenan in bata ciba iya kacin alhaji yace ta barmai gida for a while,wannan kuma bawani big deal bane a gurinta ba…….. Inda Allah ya taimaketa ma bata taba carryover ba gashi tayi nisa…………


Kawai saita fada tinanin abubuwan da batasan tinawa… “Ko ina yake yanzu?” ta tmby kanta kamar tana mgn da wani……….        Tafiya yake majestically amma bada sauri ba,wani irin perfect silence da taji ne yasa tagane maybe lecturer din ne yazo,a hankali ta dago idonta ta cikin niqab din ta kalleshi,saida taji kirjinta ya buga,tayi saurin dauke kanta………. Kasa kasa taji ta bayanta nagawa ta gefanta “shi nagani,wlh shi nake gayamiki”….. Dayar ta zaro ido tace “Da gaske?”…  Ta bayanta ta sake cewa “Wlh shine,harfa summoning courage nayi na tambeyeshi digit dinshi………. 


      “Mtseeeeww” Jinta kawai tayi taja wani uban tsaki,abinda ko magana bata tabayi a class din ba,sai wannan dan takaici da bata masan tayi ba,ba abinda ta tsana a rayuwarta irin taga mace na stooping low akan namiji dan ita bata dauki maza a bakin komai ba……. Karab  tsaki a kunnensa da duka yan class dinma sbd yanda ajin ya dau shiru,kowa ma mamaki ya dinga yi sbd tsakin ya fito sosai,gashi da niqab a fuskarta bare ace ko wani abu aka mata,barema su basu taba ganin tana magana da wani ba…….. 


    Dauke kanshi yayi daga kallon niqab din nata yace “Get up” a nitse….. Ba tare da ko dar ba ta mike dan ita kai tsaye take abu….. A nitse ya kuma cewa “Unveil!”…… Saita dago da sauri tana kallonshi ta cikin niqab din….. Kokarin controlling kanshi ya farayi dan yanzu zeyi losing kanshi,a nitse ya kuma cewa “Unveil and explain to us what cause that loud hiss?” …… Jin haka ko kowa sai ya bada attention dinshi a kanta, dama sundade a cikin curiosity dinnan,har planning suke aje a mata mgn,ana zuwa kuma sai a kasa,sun kasa gane wani irin kwarjini ne haka da ita…….Ai jitayi kamar kafafuwanta bazasu dauketa ba tsabar yanda ta kidime,ita tasan duk abunda yace Bame yiwuwa bane,amma kuma ya zatayi handling situation din,kawai sai wata dabara ta fado mata,duk da madai ba zai mata solving completely ba,ya dai fiye mata tayi unveiling a cikin mutane ta fara bayani….. “Impossible!” Ta fada a ranta…… 


    A hankali ta fara takawa zuwa stage din,dagowa yayi yana kallon ikon Allah dan as long and he’s concerned shi bece tazo gaban podium din ba,cewa yayi ta tsaya tayi bayani anan…. Saida ta karaso dab da shi sannan tadan janye niqab din yanda zaana ganin idonta kawai,ta shiga kallonshi da bold eyes dinta da suke a lumshe,tsabar saka niqab bata ko iya budesu sosai………. “Ya Salam” ya fada yana tare handout din da saura kadan su zube daga hannunshi,For once ya manta cewa he’s a psychopath! Ai be san sanda ya daka mata wani mugun tsawa ba yace “GET OUT!!”……..


Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com


Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 Author’s Contact

  • Name : Barankancy
  • Wattpad Handle : @ Unique Barakancy
  • Nick Name : 
  • Whatsapp Number : 
  • Nationality : 
  • Email :
  • Group : Noteworthy Writers Elite

The Book is free


Post a Comment

0 Comments

Ads