Maganin Rage Radadi Da Wahalar Nakuda

Mafi yawancin  mata kan fuskanci wahala da radadi a yayin da sukazo nakuda. to albishirinku shafin (kowace cuta da maganinta) ya binciko muku ingantaccen maganin wannan matsala. da za ayi amfani dashi domin haihuwa cikin sauki da izinin Allah.


Maganin Rage Radadi Da Wahalar Nakuda

 

A samu:


1. HABBATUS SAUDA COKALI 1.

2. ALBABUNAJ COKALI 1.


Adafasu da ruwa kofi guda. idan sun tafasa asauke atace asanya zuma gwargwadon yadda ake so sannan asha da duminsa.

Karanta>>> Yadda Za'a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

Idan mace tana shan wannan zata samu saukin laulayin ciki. kuma idan tazo haihuwa ma abin zaizo da sauki Bi-iznillahi.


Hakanan Idan aka samu Man Habbatus Sauda Mai kyau (Made in Saudi, ko Pakistan, ko Sudan ko egypt) tare da Man Albabunaj (Chamomile Oil) ahadasu arika sanya cokali guda acikin Shayi (Tea) ko Ruwan dumi, Idan mace tana sha zata samu sauki daga yawancin cututtukan da mata suke fama dashi kamar:


Karanta>>> Maganin Sanyi Na Maza Da Mata


* Kaikayin gaba

* Fitar farin ruwa.

* Rikicin jinin al'ada.

* Matsanancin Ciwon Mara.

* Namijin dare.

* Ciwon ciki.

* Qarancin barci.

* Daukewar sha'awa.

* Rashin ruwan nono.


Kada adauki wannan fa ida da wasa domin kuwa munba mutane da dama wannan fa idar. Sunata aiko mana da sakon godiya.


Karanta>>>Shawarwari akan yadda mace mai juna biyu zata kula da shi 

 

A turawa yan uwa su amfana


Post a Comment

0 Comments

Ads