Maganin Fibroid Da Izinin Allah

Fibroisis wata irin nau'in chutar daji ce dake tsirowa acikin mahaifar mace kuma tana haddasa manyan matsaloli ga mace. 


Maganin Fibroid Da Izinin Allah

Musamman ta bangaren rikicewar jinin al'adarta, Zubar jini marar misali, kumburin mahaifa da kuma rashin samun haihuwa.

Duk da cewa yana da wahalar magani a likitancin Bature har sai anyi aiki an yankeshi (watakil kuma ya sake tsirowa daga baya) to amma a likitancin Musulunci akwai wani hadi na musamman da akeyi domin maganceshi baki daya IN SHA ALLAH.

Ha'din kala-kala ne kuma akwai wadanda mun jarrabasu akan marassa lafiya da dama kuma anyi an dace. Ga wani nan kamar haka:

KI NEMI: Shajaratu Maryam ki jika kina sha kina chanja saiwar duk bayan kwanaki 3 har sai kinyi sati biyu kina sha.

Kuma zaki nemo:

- Garin Habbatus Sauda. 

- Garin Hulbah. 

- Garin Habbur Rashad.

Asamu Gwangwani 2 na kowanne daga cikinsu, ahada waje guda tare da Gwangwani 4 na garin Halteet.

Ki juyesu gaba daya acikin zuma ingantacciya, sannan ki zuba 15 Ci (cikin kwalbar lemo guda) na ruwan khal (Ma'u Khal) ki gauraya dukkaninsu.


Zaki rika shan cokali biyu zuwa uku bayan kin ci abinci da safe da yamma har tsawo makonni 2 ko uku, tare da shan rabin kofi na ruwan dumi bayan kinsha wannan din ko yaushe.

Zaki sha maganin nan ne bayan kin gama shan waccen saiwar (Shajaratu Maryam) din.


Bayan kinsha na sati biyu ko ukun sai ki koma asibiti a sake yi miki gwaji (Test). IN SHA ALLAHU zaki ga abun mamaki domin kuwa zaki tarar wannan fibroid din ya tafi baki dayansa.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 

Post a Comment

0 Comments

Ads