Innalillahi Yadda Wasu Magoya Bayan PDP Sukayi Hatsari Suka Mutu Baki Daya


Wasu magoya bayan jam'iyyar PDP sun rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Asabar Rahotanni sun bayyana cewa sun bayyana cewa lamarin ya faru a kusa da gadar Panyam Tawagar yakin neman zaben dan takarar gwamnan Plateau ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta yi ta'aziyya 


Magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Plateau da dama sun rasu biyo bayan hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Mangu, rahoton The Sun. An gano cewa magoya bayan suna hanyarsu na dawowa Jos ne daga wata ralli da aka yi a karamar hukumar Pankshin a lokacin da babban mota ta yi karo da su a Panyam. 


 Wani mazaunin garin Panyam, Joy Stephen, wanda ganau ne ya shaidawa The Punch a ranar Asabar cewa mutane da dama sun mutu nan take yayin da wasu sun jikkata. Stephen ya ce: "Misalin karfe 4.30 na yamma ne hatsarin ya faru. "Babban motan na dauke da yara maza da mata, suna hanyar zuwa Jos. Wadanda ke ciki magoya bayan PDP ne da ke dawowa daga ralli a Pankshin. "Amma, lokacin da suka kusa da wani gadi a Panyam, ban san abin da ya faru ba amma motar ta fadi ta kashe wasu yayin da wasu suka jikkata. An kwace wadanda abin ya faru da su zuwa asibiti a lokacin da muka isa wurin. "Hadarin abin bakin ciki ne domin an yi taron siyasan lafiya kalau." Jam'iyyar PDP ta tabbatar da afkuwar lamarin Wani sanarwa daga tawagar watsa labarai na dan takarar gwamna na PDP, mai dauke da sa hannun Manga Wamyil, da aka fitar a yammacin ranar Asabar ta tabbatar da afkuwar hatsarin.


Wani bangare na sanarwar ta ce: "Cike da bakin ciki, wani babban mota dauke da wasu magoya bayan PDP daga cikin magoya bayan dan takarar gwamna daga ralli na central zone, jihar Plateau, Pankshin, sun yi hatsari a yammaci kusa da kauyen Jwak, kafin gadan Panyam, karamar hukumar Mangu. "Mafi yawancin magoya bayan wadanda matasa ne, sun samu rauni daban-daban, yayin da wasu sun rasa rayyukansu. "Allah ya jikansu da rahama." 

Post a Comment

0 Comments

Ads