Innalillahi Akwai Kura A Gaban Iyaye Maza Da Mata Game Da Tarbiyyar Yara Karanta

AKWAI BUƘATAR IYAYE SU ƘARA JAJIRCEWA WAJEN TARBIYYAR ƳAƳANSU !!!
.
A haƙiƙanin gaskiya muna cikin wani lokaci da fitintinu suka yi yawa, wanda a yau abin tsoro ne a rayuwa cikin mu'amalat da zamantakewa ta yau da kullum, akwai abin dubawa bisa ga yadda ake samun taɓarɓarewar tarbiyya da lalacewa ga ƴaƴan musulmai da rashin ingantacciyar rayuwa na addini da amfani da ilimi wanda addinin musulunci ya ɗaura mabiyansa akai.
.
Wannan kawai idan ka kallo shi da idon basira zaka tabbatar da sakacin wasu iyayen yadda suka yi watsi da tsayawa tsayin daka wajen karantar da ƴaƴansu addinin musulunci ingantacce.
.
Idan muka duba zamu fahimci a yau iyaye sun fi bada himma da ƙoƙarin ganin ƴaƴansu sunyi karatun boko da yawa basa bada muhimmancin karatun addinin yaransu kamar yadda suke bawa karatun boko himma da jajircewa ba. Sannan ga uwa uba wajen sanya ƴaƴansu makarantin Kiristoci wanda hakan zai bada ƙarfin guiwar tasowar yara manyan gobe da ɗabi'un kafurci.


Kada kuyi mamaki ba fata ba matuƙar ba a jajirce wajen tarbiyyar yara musulmai akan turba na ƙwarai yadda addinin musulunci yayi umurni ba toh nan gaba zagi da ɓatancin da ake yiwa Fiyayyen halitta Annabi (ﷺ) daga bakin arna wataran a bakin yaran musulmai za'a rinƙa jin shi, saboda me ??? Saboda sakacin iyaye da ɗaukan ƴaƴansu suna danƙawa Kiristoci suna karantar da su.
.
Iyaye ku ji tsoron ALLAH ƴaƴa amana ne a gare ku, ku tsaya da gaske ku basu kyakykyawar tarbiyyar da zasu jiƙanku kuma su ɗaukaka kalmar ALLAH, koda zaku sanya ƴaƴanku a makarantin Kiristoci ku jajirce ku tsaya musu ku rinƙa karantar dasu addini acikin gidajen ku kuma ku sanya su isalamiyya, ku karantar dasu Alƙur'ani ingantacce karatu da sanin hukuncinsa da ma'anoninsa.
.
Wani magabaci yake cewa: “Wannan alʼummar ba zata gushe ba cikin alkhairi, matuƙar tana koyawa ƴaƴanta Alƙur'ani.” [Abdallah Bin Isa, Kitabul Iyal Li Ibn Abid-dunya: 309]


Alƙur'ani yana da tasiri matuƙa wurin kafa Imani a zukatan yara masu tasowa, Allah yakarawa mana Albarka. 
®M

Post a Comment

0 Comments

Ads