Hisbah Za Ta Debi Sabbin Dakaru 3,100 A Kano

 Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince wa Hukumar Hisbah ta Jihar ta debi sabbin dakaru 3,100 a Kananan Hukumomin Jihar 44.Babban Kwamandan Hukumar a Jihar, Dokta Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan, kamar yadda Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya sanar.

Ibn Sina ya kuma ce kaso 80 cikin 100 na mutanen da za a diba za su kasance maza ne, sau kuma mata kaso 20.

Sai dai ya ce za a raba adadin da za a diba ne ga dukkan Kananan Hukumomin Jihar, inda ya ce kaso 70 cikin 100 na wadanda za a diba za su kasance cikin dakarun hukumar da aka dauka kwanakin baya, sai kuma ragowar 30 din da za su zama sabbin diba.

A bara ne dai Gwamnan na Kano ya amince da dibar dakaru 5,700 ga hukumar.

Babban Kwamandan hukumar ya shawarci dukkan masu neman gurbi a hukumar su tuntubi Kananan Hukumominsu na ainihi.

Source: Aminiya Dailytrust

Post a Comment

0 Comments

Ads