An yi ram da wasu maza 4 bayan sun taru sun yi wa kadangare fyade

 Wasu maza 4 suna hannun hukuma bayan an zargesu da yi wa wani kadangaren gadi a Gidan kulawa da Damisa na Sahudari da ke Maharashthra a kasar Indiya, Instablog ta ruwaito.Kamar yadda rahotanni suka nuna, mazan guda 4 mafarauta ne, cikinsu akwai Sandeep Tukram, Pawar Mangesh, Janardhan Kamteka da Akshay Sunil.

Hukuma ta yi ram da su ne bayan an duba bayar daya daga cikinsu an ga bidiyonsu suna lalata da kadangaren.

Bidiyon da CCTV ta nade daga wani bangare na dajin Maharashtra ya nuna yadda mazan 4 suka shiga bangaren kulawa da Damusar na Sahyadri wanda gwamnatin kasar Indiya ta gina a 2008 musamman don adana damusoshi.

Da farko mai gadin dajin ya kama daya daga cikinsu amma sauran sun tsere. Daga bisani ne aka kama su a kauyen Hativ a yankin Ratnagiri da ke Maharashtra.

Mai kulawa da dajin ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun Indiya don sanin hukuncin da za a yanke musu.

Source: LabarunHausa

Post a Comment

0 Comments

Ads