Alamomin Matsalar Fibroid

 Mene ne "Fibroid ?"

Alamomin Matsalar Fibroid

Fibroid: wata matsalace a mahaifar mace, wato wani curin nama ne yake fitowa mace a mahifarta kuma yana girma a mahaifar. Ƙululun naman Yana iya fitowa fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.


KARANTA WANNAN>>> Haɗin Mai Da Tsohuwa Yarinya..


ALAMOMIN MATSALAR FIBRIOD

Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:

1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci.

2. Zubar jini a baaƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila.

3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa.

4. Yawan fitsari.

5. Ciwon baya daga ƙasan baya.

6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i.

7. Rashin jini saboda yawan zubar jini.

8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki.

9. Basur mai sa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya.

10. Ciwon ƙafa.

11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma.

12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani.


MENE NE KE KAWO MATSALAR FIBROID?

Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod.


KARANTA WANNAN>>> Amfani 15 Da Ganyen Lansur Yake Yi..


 Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i.


A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ƙwayoyin halitta (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. 


A taƙaice, ESTROGEN shi ne sinadarin da faibirod suka dogara da shi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.


KARANTA WANNAN>>> Amfanin Zogale 18 Da Ba Kowa Ya Sani Ba..


WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:


Gaado: Idan mahaifiyarki ko ƴar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.

Jinsin baƙar fata: Mutanen Africa ko ƙasashen bakar fata, wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baƙar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.

Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), ƙiba, ƙarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shangiya da sauransu.


Maganin Fibroid Da Izinin Allah


Post a Comment

0 Comments

Ads