Adam zango naciga da karbar suka akan Rungumar da yay a fim din Asin da Asin.


 A satinnan batun nunin da aka nuno Adam A Zango a cikin shirin asin da asin ya rungumi jaruma Meera shu’aibu ya tada kura wanda har maganganu da sukayi yawa Adam Zangon ya fito yayi wani video da ya nuna yadda suka sanja jarumar da wani namiji maimakon ta Wanda mun kawo muku videon.


Sai dai wannan zamewar da Adam A zango yay bata zama uzuri i wajen wasu ba domin a cewar su sakon da ya isar shine mai muhimmanci ba yadda aka yi wajen isar da sakon ba. Duk wanda yaga wancan video bai kuma ji jawabina ba zai tsamanin kamar na rungumi mace ne cewar jarumin.


Wasu na korafin ai ba’a rabu da bukar ba an haifi habu, Kamar yadda rungamar macen yake haramun haka zalika namiji ya sa kayan mata ma shima haramun ne. kamar an gujewa wani haram din ne an fada wani.


Da yawan mutane sun dauki wannan dauka suna dorawa akan kafar sada zumunta suna allah wadai akan batun.


Malamin nan na TikTok Abu safiyan shima ya bayyana ra’ayin sa akan wannan dauka.

Post a Comment

0 Comments

Ads