Mijina Ba Ya Iya Biyamun Bukatana Kwata-Kwata, Wata Mata Ta Amince A Raba Aurensu Da Angonta

 Wata Kotun da ke Mapo a garin Ibadan, na Jihar Oyo, ta dage sauraren karar da wani mutumi mai suna Imma Wole ya shigar a gabanta a kan matarsa, mai Olu Wole bisa zarginta da yi masa rashin kunya da rashin da’a a zaman su na aure.

Tribune ta ruwaiti cewa, Mai shigar da karar ya kara da cewa wanda ake tuhumar ta saba zaginsa a bainar jama’a da kuma fada da shi da makwabtasa.

Imma ya shaida wa kotu cewa ya gaji da zaman aure da Olu saboda babu sauran soyayya a tsakaninsu. Related Articles

Ya roki kotu da ta hana matarsa ​​daga cin mutuncinsa da kuma yi masa barazana.


 Olu ya amince a raba auren, inda ya bayyana cewa Imma da danginta ba su yarda ta sami kwanciyar hankali ba tun da suka yi aure.


 Ana ta bangaren Wadda ake karar ta bayyana cewa ta dade tana juriyan zama a rayuwarsu ta auren saboda mijin nata ba shi da karfin jima’i kuma ya kasa gamsar da ita a dakin kwananta.


 Imma ya bayyanawa Kotu cewa: “Ya shugabana, ba na son matata kuma. Ina rokon wannan kotu mai daraja da ta raba auren mu.


 “Olu ba ta ganin mutunci na. Ta iya hada kafada da ni a cikin gidana, kuma ta ki bin umarnina a lokacin da take so.


 “Matata ta kasance tana barin gida ba tare da yardara ba kuma ba za ta sanar da ni game da inda ta je ba.


 “Olu wani lokaci yakan kasance ba ya gida na mako guda ko fiye kuma ya kasa bayar da wani gamsasshen bayani idan ta dawo.


 “Tana ɗaga muryata a kaina a duk lokacin da na nuna rashin jin daɗina game da rashin ɗa’ar kuma wani lokacin takan yi fada da ni.


 Ita kuwa Olu ta bayyanawa Kotun cewa , “Ya shugabana, na haƙura da aurenmu. Na yarda ni da Imma mu rabu.


 “Mijina da danginsa sun ƙi su bar ni na huta. Danginsa ba su daina tsoma baki a harkokinmu auren mu ba.


 “Ni da Imma kullum muna cikin rigima domin ya kasa sauke nauyin da ke kansa na aure a kaina.


 “Ban ji dadin aurenmu ba saboda Mijina bai da karfin jima’i kwata kwata. Ya kasa gamsar da ni a gadon.”


 A karshe dai mai Mai shari’ar kotun, Mrs S.M Akintayo, ta dage sauraron karar bayan ta saurari bangarorin biyu.


 Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ja kalubalanci jam’iyyar PDP idan ta isa ta kore shi, suga mai zai biyo baya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

 Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da sabon titi a jihar Rivers.
Post a Comment

0 Comments

Ads