Gobara ta kashe mutum 19 a Afghanistan: Da Kuma yadda al'amari ya kasance

 Gobara ta kashe mutum 19 a Afghanistan

Gobara ta kashe mutum 19 a Afghanistan: Da Kuma yadda al'amari ya kasance


Akalla mutum 19 sun rasa rayukansu a 

Afghanistan yayin da wasu da dama suka jikkata a wata gobara da ta tashi a hanyar karkashin kasa da ke.


Jami'an Taliban sun ce wata tankar mai ce ta haddasa wutar a kan titin da ke zuwa Kabul.


Wutar ta bazu inda ta kama wasu motocin da ke bi ta hanyar.


Mata da yara na cikin wadanda suka rasa ransu a gobarar.


Wakilin BBC ya ce motocin daukar marasa lafiya sun kwashi wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci mafiya kusa, kuma akwai yiwuwar adadin wadanda lamarin ya shafa ya karu.


Wasu hotunan da aka wallafa a kafafan sada zumunta sun nuna yadda motoci suka kone ƙurmus.

Abin dai ya munana matuka sai dai ace ALLAH say Kaka Amen 🤲

Post a Comment

0 Comments

Ads