Zamfara: An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Zamfara

A cikin yan shekarun nan Garkuwa da mutane ya zama ruwa dare a Arewacin Najeriya

Kusan kullin sai an sace mutane don karban kudin fansa musamman a Arewa maso yamma


An yi awon gaba da wasu Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu yan jihar Zamfara yayinda suke hanyar dawowa daga jamhurriyar Nijar ranar Juma'a, 11 ga Satumba, Premium Times ta ruwaito.


An sace Alkalan, Sheikh Sabiu Abdullahi da Sheikh Shafi'i Jangebe, ne yayinda suke hanyarsu ta komawa Zamfara bayan halartan wani taro da suka yi a Nijar.


Malam Sabi'u Abdullahi ne na'ibin limanin Masallacin Juma'an Usaimin dake Gusau.


Abokinsa, babban limanin Masallacin Umar bin Khaddab dake Gusau, Sheikh Umar Kanoma, ya tabbatar da hakan a hudubar Juma'a.

"Muna baran addu'a daga al'ummar Musulmi kan Alkalai biyu da aka sace yayinda suke hanyar dawowa daga Maradi a jamhurriyar Nijar," Yace.

Limamin ya yi kira da gwamnatoci su kare rayukan mutane da dukiyarsu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, bai amsa kiran waya da sakonnin da aka tura masa ba.

Post a Comment

0 Comments

Ads