Yawan Bashin Da Ake Bin Nigeria Ya Kai Kimanin Trillions 31

 


Yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai sama da naira tiriliyan 31 daga ƙarshen watan Yuni, kamar yadda ofishin kula da basusuka a Najeriya ya sanar.


Ofishin ya bayyana a cikin rahoton da ya fitar ranar Laraba cewa yawan bashin ya ƙaru da naira tiriliyan 2.38 tsakanin wata uku.

Yawan bashin ya shafi wanda jihohi da gwamnatin tarayya suka karɓo.

"Alƙalumman sun nuna cewa a naira - jimillar bashin na gwamnatin tarayya da jihohi 36 haɗi da Abuja ya kai naira tiriliyan 31.009 kwatankwacin dala biliyan 85.897.

Bashin ya ƙaru ne saboda rancen dala biliyan 3.36 da gwamnati ta karɓo daga asusun lamuni na duniya IMF da kuma rance daga cikin gida don tallafawa kasafin kuɗi na shekarar 2020 da aka sabunta.

Daga ƙarshen 2015, bashin naira tiriliyan 12.12 ake bin Najeriya, makwanni bayan hawan gwamnatin APC ta shugaba Buhari.

Hakan na nufin tsakanin shekaru biyar na mulkin Buhari, bashin Najeriya ta ƙaru da kusan tiriliyan 19. Ofishin kula da basussuka a Najeriya ya ce yawan bashin zai ƙaru yayin da ake jiran kuɗaɗen rance daga Bankin Duniya da Bankin raya Afirka da kuma Bankin musulunci domin tallafawa kasafin kudin Najeriya na 2020 musamman wanda ƙasar ta nema sakamakon tasirin annobar korona.

Haka kuma kuɗaɗen da ake bin jihohi zai ƙaru daga sabon rancen da suka nema.

Post a Comment

0 Comments

Ads