Yadda Yan Sandar Jahar Katsina Sukayi Nasara Kama Shahararen Mai Garkuwa Da Mutane

Rundunar Yansandan Jahar Katsina tayi Nasarar Chafke wani Mai Garkuwa da Mutane tareda Kubutar da Mutanen da yayi Garkuwa dasu....
Mai Magana da Yawun Rundunar Yansandan Jahar Katsina SP Isah Gambo ya bayyana cewa a ranar 08/09/2020 da Misalin karfe Biyar da Mintuna Hamsin 17:50hrs, Rundunar ta samu ingantattun bayanan sirri Inda sukayi Nasarar Chafke wani Mai suna Abubakar Ibrahim, Dan Kimanin Shekaru Goma Sha Tara 19 daga Dajin Rugu dake Karamar Hukumar safana ta jahar Katsina.

Shi dai Wannan Dan Ta'addar yana daga cikin Barayin dajin da suke addabar Yankunan Safana, Batsari, Danmusa dama Karamar Hukumar Kurfi Duk a cikin jahar ta Katsina.

Ya kara da cewa a ranar 03/09/2020 da 07/09/2020 wanda ake zargin ya jagoranci tawagar shi akan Babura kowannesu dauke da Bindiga kirar AK 47 inda suka kai hari a kauyen Dagarawa da Kudewa a karamar hukumar Safana da Kurfi Inda sukayi nasarar sace Ashiru Ibrahim, Dan Kimanin Shekaru 32 a Kauyen Dagarawa safana sai kuma Duduwa Audu, Yar Kimanin Shekaru Hamsin 50 da kuma Asiya Saleh, Yar Kimanin Shekaru Arba'in da Biyar 45yrs dukkan su daga kauyen kudewa Karamar Hukumar Kurfi inda suka dauke su zuwa Dajin Rugu.


Sai dai Rana ta baci ga wanda ake zargin domin ya fada komar Jami'an tsaron Runduna ta Musamman masu kula da Yan Fashi da Makami ta SARS bayanda ya karbi kudin fansa Naira Dubu Dari Biyu da Arba'in da Daya (N241,000:00k) daga hannun Yan'uwan wadanda aka sata din.

Yayin binciken Yansanda wanda ake zargin ya amsa laifinsa hadin guiwa da wasu da yanzu haka make nema ruwa a jallo, kazalika Kuma an samu kudin da ya karba a Matsayin kudin fansa a tare dashi Naira Dubu Dari Biyu da Arba'in da Daya da Dari Biyu (N241,200:00K)Rundunar tayi Nasarar Kubutar da Wadanda akayi garkuwa dasu an kuma mikasu ga danginsu bayan da Likitochi suka su a Babban Asibitin Garin Kurfi.

DAGA Muhammad Aminu Kabir

Post a Comment

0 Comments

Ads