Yadda Wata mota ta buge Kunkuru ɗan shekara 75 a jihar Kebbi

 Wata mota ta buge Kunkuru ɗan shekara 75 a jihar KebbiBabban asibitin dabbobi na jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo dake jihar Sokoto, ya karbi wani majinyacin Kunkuru da mota ƙirar Hilux ta kaɗe a garin Argugun na jihar Kebbi.
Kunkurun mai shekara 75, ɗaya daga cikin likitoci da suka yi wa kunkurun aiki ya tabbatar wa Hausa Daily Times cewa Kunkurun ya samu rauni a baya, inda motar ta takashi har ya fashe.


Ya kuma bayyana cewa, majiyacin ya samu kulawar likitocin hadin gwiwa daga asibitin dabbobi da kuma bangaren fiɗa na asibitin koyarwa na UDUTH kuma an yi nasarar ceto rayuwar Kunkurun.

Post a Comment

0 Comments

Ads