Yadda Tsawa Ta kashe Mutane Uku Yan Gida Daya A Jihar Katsina


Rahotanni daga jihar Katsina na cewa Mutane 3 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tsawa dsta fads musu yayin ruwan sama.
Lamarin ya farune a kauyen Kukar Gesa dake jihar Katsina, wadanda suka mutun duka ‘yan Gida dayane kuma mahaifinsu, Malam Musa Danladi ya tabbatar da rasuwarsu inda yace 2 daga cikin ‘ya’yansa ne 1 kuma jikansa ne.
Su 5 suka fake a karkashin wata bishiya yayinda ake ruwan inda a nanne tsawar ta fada musu da misalin karfe 5 na yammacin Asabar yayin da suka je girbar Gero gonarsu.

Bayan da aka ji shiru ne sai aka fara neman mutanen inda aka je aka tarar da gawar 3, 2 kuma na kwance suna jinya, an garzaya da wanda suka jikkata Asibiti yayin da wanda suka rasu kuma aka yi jana’izar su kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Post a Comment

0 Comments

Ads