TURKASHI: Kwanon Kanzo Yayi Tashin Gwauron Zabo A Nigeria Daga 170 Zuwa Naira 700

 TURKASHI: Kwanon kanzo ya kai Naira 700 a Nigeria


...a baya ana sayar da kwano guda akan Naira 150 ko 170 ne

Daga Manuniya

Anya lokaci bai yi ba da za a bude boda domin talaka ya samu saukin rayuwa a Nigeria?


Duk hakurin da za a cewa mutum yayi tabbas ba zai iya hakurin cigaba da zama da yunwa ba. Babu shakka garin rogo da kanzo sune abinci mafi sauki da talakan Nigeria zai iya fafutuka ya samu domin tsira da rayuwarsa.


Sai dai wani abun tada hankali shine yadda binciken Manuniya ya gano yanzu haka shi kanshi kanzo yayi tashin gwauron zabi wanda hakan ke nuna shima zai gagari talaka.


A baya ana sayar da kwanon kanzo Naira 150 ko N170 amma a yanzu ya haura N700 duk kwano daya sannan ma dai mutum yayi odarsa tunda wuri idan yana so


Wakilin mu Bilyaminu da ya je sayo kanzo wajen kwastomansa Malam Tanko Sokoto wani fitaccen dan kasuwa mai sayar da kanzo ya fadawa wakilin namu cewa


"Koda na je jiya sayan kanzo na tarar da buhu biyu na kanzo jingine amman ya ce wallahi an sayar, ya ce ai yanzu duk mai son sayen kanzo to sai yayi booking (bayar da oda) din sa yake samun sa, yanzu haka buhu biyar na kan hanya in har kana so kayi booking, ma'ana ka kawo kudin ko kwano kake so, saboda ya zan da an kawo a ajiye maka."


"Kwanon kanzo yanzu ya kai Naira dari bakwai (700) ko kwandala ba'a rage maka. In baka saye bada wuri." Inji Malam Tonko Sokoto


Muna rokon Allah ya kawowa talakan Nigeria sauyi mai kyau mai inganci wanda zai sanya ya samu saukin rayuwa.

Post a Comment

0 Comments

Ads