Turkash! An sace motar da aka bawa bakanike gyara yayin da ya tafi gidan karuwai da motar

Wani bakanike ya shiga tasku bayan an sace motar kwastomansa da ya bashi gyara a yayin da ya tafi otel ganin karuwarsa


Karuwar ta tabbatar bakaniken ya yi tatil da giya sannan ta kira wasu maza da suka hada baki da ita suka shigo dakin suke dauke makulin motar suka tsere


Daga bisani bayan makaniken ya farka bai ga makuli ba kuma babu mota sai ya garzaya ofishin yan sanda ya yi korafiWani bakanike da ke Lafia a jihar Nasarawa, John Simon, ya batar da motar kwatomansa a yayin da ya shiga gidan wasu karuwai a sabon yankin Nyanya.


City Round ta gano cewa, Simon na tsaka da shakatawarsa da wata karuwa mai suna Stella Emeerga yayin da wasu mutane uku suka hada kai da ita wurin sace motar kirar Toyota Camry.


An gano cewa, Simon mai 'ya'ya biyu, ya tsaya a gidan karuwan yayin da zai wuce Abuja domin kai wa kwastomansa motar da ya gyara.


Bayan mankas da yayi da giya, daya daga cikin barayin ya shiga cikin dakin inda ya dauke makullin motar da ke ajiye a kasa.


Bayan ketowar alfijir, bai ga makullin motar ba kuma bai ga motar a inda ya ajiye ta ba. Simon ya garzaya ofishin 'yan sanda da ke Sabuwar Nyanya inda ya kai rahoto kuma aka damke sa tare da Emeerga.KARANTA: Wata Sabuwa: Adam Zango Ma Ya Nemi Talakawa Su Hada Mishi Dari Biyar-Biyar Yayi Wa Atiku Waka


Bayan watanni da aka kwashe ana bincike amma babu nasara, mai motar ya mika korafin da gaban sifeta janar na 'yan sandan Najeriya inda aka mika lamarin hannun runduna ta musamman.


A cikin kwanakin nan aka damke daya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Monday Francis.


Wanda ake zargin mai shekaru 30 ya ce hada kai suka yi da Emeerga wurin satar motar tare da wasu 'yan kungiyarsa wadanda basu shigo hannu ba har yanzu.


Ya ce, "mu hudu ne muka hada kai tare da Emeerga wurin satar motar daga direban bayan isowarsa gidan karuwan. Mun shirya bayyana cewa Stella bata da hannu a ciki. Na kwankwasa kofa a kan cewa ina bukatar ruwan sha sai ta fito ta kawo min yayin da daya daga cikin mu ya shige ya dauke makullin motar


"Stella ta sanar da mu cewa ya bugu amma za mu iya gwadawa. Dodo da Ezekiel ne suka tafi da motar. Sun kai wa wani wanda zai siya amma ya tsere."


Amma Emeerga mai shekaru 25, ta ce Simon kwastomanta ne na kusan shekara daya, amma ta musanta hada kai da masu satar motar.


Ta ce bata san cewa an sace motar ba har sai zuwa safe da ta ga an cire wani tsumma da take rufe kofarta da shi.


A yayin bayyana yadda lamarin ya faru, Simon ya ce ya san Emeerga ta bar dakin amma bai yi tsammanin wani mugun abu suka shirya ba.


"Ni bakanike ne kuma direba. Kwastomana ya kira ni daga Abuja a kan cewa in kai masa motarsa amma sai na tsaya a wurin Stella. Na san ta kusan shekara daya.


"Ban san cewa wani ya shigo dakin ba. Na ga fitar ta amma ban tashi ba. Ta dawo inda muka kwana muna more juna amma daga baya mun yi bacci. Da na tashi ne na ga babu makullin motar."

Post a Comment

0 Comments

Ads