To Fa! Wani Mutum Ya Auri Uwar Matarsa Bayan Sun Rabu Da Matar Tashi

 - Wata mata mai suna Brenda ta auri tsohon mijin 'yar ta mai suna Clive a garin Warrington da ke yankin Cheshire na kasar Ingila bayan ya saki 'yar ta


- Da farko dai hukumomin kasar sun hana su aure domin akwai dokar da ta hana auren surukai amma daga bisani an sauya dokar kuma suka yi aurensu


- Ma'auratan sun ce suna fuskantar tsangwama daga 'yan uwansu har ta kai sun kaurace musu amma hakan bai dame su ba


Wani mutum mai suna Clive Bunden da matarsa Brenda daga Warrington, Cheshire a Ingila sun shafe kimanin shekaru 30 suna zama tare duk da cewa ya taba auren 'yar ta Irene a shekarar 1977.


The Mirror UK ta ruwaito cewa sun fi shekaru 30 suna tare duk da cewa shekarun su 13 da aure duk da irin alakar da ke tsakaninsu.


Da farko hukuma ta kama shi a lokacin da ya nemi surukarsa ta aure shi domin hakan ya saba wa dokar kasar. Sai dai daga bisani sun yi aure bayan an sauya dokar a shekarar 2007.


"Mutane ba su yi tsamanin za mu dade tare ba amma gashi har yanzu kullum sai kara shakuwa muke yi," a cewar Clive mai shekaru 65.


"Muna tare a kowanne lokaci, abin gwanin ban mamaki"A shekarar 1977 suka yi niyyar yin aure. Amma kwanaki kadan bayan sun sanar da ranar aurensu a kotun garinsu na Warrington, Cheshire sai aka kama Clive.


An fada masa cewa akwai wata doka da ta hana mutum ya auri surukarsa kuma za a iya masa daurin shekaru 7 idan ya aure ta.


Saboda mijin Brenda na farko, Richard ya rasu sannan Irene ta sake aure, sun yi tsammanin babu matsala za su iya yin aure.


Shi Da Uwar Matarsa 

Bayan haka ne Clive ya fara fafutikan ganin an canja wannan dokar da aka kafa shekaru 500 da suka shude.


Sai bayan shekaru 10 sannan wata kotu a Turai ta soke haramcin auren surukai.


"Na tuna lokacin da muka ji labarin a talabijin a Satumban 2005,"  in ji Clive.


"Nan take na tsuguna na ce Brenda ta aure ni. Idanu na cike da hawaye."


A ranar 17 ga watan Maris na 2007 aka daura musu aure a kotun da Clive ya auri Irene shekaru 30 da suka gabata.


Mafi yawancin iyalansu ba su hallarci daurin auren ba ciki har da Irene. Wani dangin su ne nesa ne kawai ya aiko musu da katin taya murna.


Brenda ta ce 'yan uwan mu ba su cika ziyarar mu ba amma hakan bai dame mu ba domin abinda ke da muhimmanci wurin mu shine kasancewarmu tare.


Clive ya ce hankalinsa ya fi kwanciya bayan an daura musu aure.

Post a Comment

0 Comments

Ads