To fa! Mutum Mafi Muni A Duk Fadin Duniya Ya Auri Mace Ta Uku (Hotuna)


Bahaushe yana cewa so gamon jini, tabbas hakan ya tabbata a kan wani mutum wanda ake cewa yafi kowa muni a duniya. Godfrey Baguma mai wasan bada dariya ne a kasar Uganda, kuma an fi saninsa da Ssebabi. Mafi munin mutumin a fadin duniyar ya aura masoyiyarsa a matsayin mata ta uku a wani irin kasaitaccen biki mai cike da shagali. 

An daura auren masoyan inda suka zama mata da miji. Babu shakka suna cike da farin ciki inda suka dinga daukar hotunan da suka karade kafafen sada zumuntar zamani. Godfrey Baguma, mai shekaru 47, yana fama da wani irin ciwo ne wanda har yanzu ba a gano kansa ba.


A shekarun da suka gabata, matarsa ta biyu mai suna Kate Namanda mai shekaru 30 ta haifa yarinya mace. Baguma ya samu nasarar lashe wata gasa a 2002, bayan ya shigeta domin samarwa iyalansa kudi, jaridar The Nation ta wallafa.Kafin aurensa da Kate, Godfrey yana da mata daya da yara biyu, amma auren ya rabu bayan da ta kama shi yana cin amanarta. Ssebabi yana da 'ya'ya bakwai. Ya samu sunansa Ssebabi bayan nasarar da yayi wurin lashe gasar zama mutum mafi muni a duniya. Yana rayuwa a Kyawanga da ke yankin Lwengo, kuma yana da 'ya'ya biyar da Kate Namande.

Post a Comment

0 Comments

Ads