Satar Dan Akuya Ta Sanya An Daure Wani Magidanci Daurin Shekaru Uku A Gidan Yari

 Satar Dan Taure Ta Sanya An Daure Wani Magidanci Daurin Shekaru Uku A Gidan Yari


Wata kotun majistare da ke garin Kwadon a jihar Gombe ta aike da wani manomi mai kimanin shekaru 28 a duniya zuwa gidan yari bisa laifin satar dan taure.


An dai gurfanar da manomin, mai suna Aliyu Buba mazaunin Garin Waziri na karamar hukumar Yamaltu Deba na jihar ne bisa zargin keta iyaka da kuma sata.


Rahotanni dai na nuna cewa mutumin ya aikata lafin ne da misalin karfe biyu na daren 12 ga watan Agusta, inda ya balle gidan wani mai suna Tela Yahaya sannan ya saci wani dan taure da darajarsa ta kai kusan N10,000.


Mutumin dai ya amsa laifin da aka zarge shi da shi.

Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Kofur Abba Mathias ya shaidawa kotun cewa laifin ya saba da sashe na 286 na kundin dokar penal code.


Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Bala Ciroma ya aike da mutumin zuwa gidan yari na tsawon shekaru uku ko kuma biyan tarar Naira dubu dari biyu.

Kazalika, kotun ta kuma umarce shi da ya biya mallakin dan tauren N15,000.

Post a Comment

0 Comments

Ads