Rarara Ya Tara Million 57 Cikin Kwana Biyu Kacal Bayan Da Ya Nemi Talakawa Su Tura Dubu Dubu

Kwana 2 da fara neman karo-karo din Naira DubuDubu daga masoyam shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Tauraron mawain shugaban kasar, Dauda Kahutu, Rarara ya tara Miliyan 57.
Wata Majiya ta bayyanawa Sahara Reporters cewa mawakin ya tara makuda kudadenne daga masoyan shugaban kasar da suka ta tururuwar aika masa da kudin.

Rarara dai yace ba zai sakewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari waka ba har sai idan masoya shugaban kasar ne suka tara masa kudin yin wakar kuma ga dukkan alama masoyan shugaban kasar sun amsa kira.

Post a Comment

0 Comments

Ads