NNPC: Nan Gaba Kadan Talakawa Zasu Gane Janye Tallafin Mai Alkhairi ne


 A karon farko tun bayan janye tallafin man fetur a Najeriya, kamfanin mai na kasar NNPC, ya fito ya mayar da martani ga masu sukar matakin, inda ya ce masu hannu da shuni ne ke amfana da tallafin ta hanyar yin cuwa-cuwar data wuce kima.

Shugaban kamfanin na NNPC, Malam Mele Kyari, ya shaida wa BBC cewa nan gaba talaka zai ci ribar janye tallafin.

''Talaka sam bashi ke cin ribar janye tallafin ba, idan aka yi la'akari da cewa shi talaka ba kowa ke da abin hawa ba, amma masu hannu da shuni su ke da motoci da dama.

Ya ce don haka masu kudin suke cin ribar wannan tallafin man, don haka bisa la'akari da yadda talaka kullkum shi ke shan wahala shi ya sa aka janye tallafin.

" Idan har ba a janye tallafin man ba, to ko shakka ba bu talaka zai ci gaba da shan wahala, kuma gwamnati ba zata iya yin wasu ababan more rayuwa ga al'ummarta ba". Inji Malam Mele Kyari.

NNPC

Shugaban na NNPC ya ce,"Na san cewa wannan janye tallafin man nan gaba za a ga amfaninsa, kuma amfanin da ba a samu ba a baya, to a yanzu za a same shi".

Ya ce dangane da batun karin farashin man fetur kuwa abubuwa biyu ne za su faro.

Na farko " Zai rage sata wadda manya ke yinta, sannan na biyu abubuwan da ake son yi da ba a samu dama ba da karin farashin man za a iya yin su".

Ya ce talakawa su zuba ido su gani kafin nan da shekara uku masu zuwa zasu ga amfanin janye tallafin man fetur da kuma karin farashinsa.

Malam Mele Kyari, ya ce a yanzu mutane na ganin kamar an jefa su cikin wani kangin rayuwa, sai dai da sannu za su ga amfanin wannan kari na mai.

Ya ce, hatta matatun man da suka lalace ko suka daina aiki a Najeriya, da wannan kudi da aka kara duk za a gyarasu, baya ga kuma sauran ababan more rayuwar da gwamnati zata gina ko ta samar don al'umnmarta, kamar makarantu da asibitoci da tituna da dai makamantansu.

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da janye tallafi man fetur, jama'a ke bayyana mabambantan ra'ayoyi inda wasu ke ganin cewar matakin ya kara jefa talaka cikin mawuyacin hali.

Post a Comment

0 Comments

Ads