Ni Ba Yarinya Bace Dan Haka Ni Matar Manya Ce Ba Yara Ba Inji Rashida Mai Sa'a

 Ni Matar Manya Ce – Rashida Mai Sa’a

Jarumar fina-finan Hausar nan Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Mai Sa’a, kuma tsohuwar mai bai wa gwamnan Kano shawara ta ce, ita matar manya ce ba matar yara ba.

A wata tattaunawa da jarumar ta yi da Freedom Radio da ke birnin Kano, kan wani matashi da ya aike mata da saƙon soyayya ta shafin Facebook ta ce, ita ta wuce ajin yara sai dai manya kuma ita mai tashe ce har yanzu.

Jarumar ta ce, “Wannan yaron ni da shi mun yi magana ya ce, shi masoyi na ne, amma na faɗa masa bai kamata ya dinga haka ba, ni ba ta yau ba ce, ba kuma yarinya ce ƙarama ba, kuma ni ba ta yara ba ce, matar manya ce, ka kalli mai sa’a mana?”.

A baya-bayan nan ne matashin mai suna Musa Rafin Kuka ya wallafa wani bidiyo a shafin sa na Facebook wanda cikin sa ya nemi afuwar jarumar bisa rashin kunya da ya ce, ya yi mata.

Freedom Radio ta tuntuɓi Musa Rafin Kuka inda ya ce ya samu yin magana da Rashida Mai Sa’a bayan da ya wallafa saƙon cewa ya riga ya kamu da ƙaunarta, amma ta nusar dashi cewa bai kyauta mata ba, kuma tuni ya nemi afuwar ta.

Wannan batu dai ya ɗauki hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta da dama waɗanda suka riƙa yin tsokaci a kai.

Post a Comment

0 Comments

Ads