Lalata: Daga Dawowa Makaranta An Cafke Malami Yana Lalata Da Daliba Mai Rubuta Jarabawa


Daga dawowar dalibai makaranta, wani Malami ya zakkewa daya daga cikin dalibansa 

- Gwamnatin jihar Ogun ta amince da bude makarantun firamare da Sakandare


Tuni an damke Malamin kuma an kai yarinyar Asibiti Wani Malami a jihar Ogun, Matthew Adebayo, ya shiga hannun yan sanda kan laifin lalata daliba mai zana jarabawar kammala karatun sakandare WAEC a makarantar da yake karantarwa. Jaridar City Round ta samu labarin cewa an damke Adebayo ne bayan mai makarantar ta kai kararshi ofishin yan sandan Sango.

An tattaro cewa dalibar makarantan kwanan yar shekara 16 ta kai karan Adebayo wajen shugabar makarantan cewa ya dade yana lalata da ita cikin aji da daddare. Malamin ya yi mata barazanar cewa za ta fadi jarabawa idan bata amince masa ba. Kakakin hukumar yan sanda jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da damke Adebayo a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Yace: "Hukumar yan sandan Ogun ta damke Wani malamin makarantan kudi (an sakaye sunan makarantan), Mathew Adebayo, kan laifin lalata wata dalibar makarantar yar shekara 15."

"An damke Malamin ne bayan shugabar makarantan ta kai kararshi ofishin yan sanda Sango cewa daya daga cikin daliban SS3 yana lalata da ita tun lokacin da aka koma makaranta don rubuta jarabawan WAEC.


"Ta bayyana cewa Malamin ya yiwa dalibar barazanar cewa ba za tayi nasara a jarabawar WAEC dinta ba idan bata amince masa ba, saboda haka yana kaita cikin aji da dare inda yake zakke mata."

Kakakin ya ce yarinyar ta kai kara ne saboda ta fara gajiya da abinda Malamin ke yi mata. Ya kara da cewa, "Tuni ya tabbatar da cewa ya aikata laifin kuma tuni an garzaya da ita asibiti."

Legit ta ruwaito muku cewa gwamnatin jihar Ogun ta sanar da ranar da dalibai zasu koma makaranta bayan watanni biyar da zama a gida sakamakon bullar cutar Korona. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa daliban jihar zasu koma karatu fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020 amma ba kamar yadda aka saba ba, TVC ta ruwaito.

A sabon tsarin, daliban firamare aji 1 - 3 zasu yi karatu daga karfe 8 zuwa 11 na safe. Sannan daliban aji 4 zuwa 6 su fara karatu daga karfe 12 zuwa 3 na rana. A bangaren makarantun sakandare, daliban ajin JSS1 zuwa JSS3 zasu yi karatu daga karfe 8 zuwa 11 na safe, sannan daliban ajin SS1 zuwa SS3 zasu yi daga karfe 12 zuwa 3 na rana.

Source: Legit.ng

Post a Comment

0 Comments

Ads