Kunkuru Mai Shekara 80 Da Mota Ta Taka Ya Mutu Bayan Anyi Masa Tiyata

Kunkurun nan mai kusan shekara 80 da likitocin dabbobi a Sokoto da ke arewacin Najeriya suka yi wa tiyata bayan mota ta taka shi a Argungu ya mutu.Kunkurun ya mutu ne ranar Juma'a da la'asar, a cewar shugaban likitocin dabbobin yankin Argungu, Dr Samiru Ladan Argungu.

Dr Samiru, wanda shi ne ya soma bai wa kunkurun kulawar gaggawa kafin a kai shi Sokoto, ya shaida wa BBC cewa kunkurun ya mutu ne sakamakon rashin kulawa bayan an koma da shi Argungu daga Sokoto inda aka yi masa tiyata.

A cewarsa, kunkurun, wanda mallakin Alhaji Sulaiman Jarma, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi ne, ya cika ne saboda "yaron da ya kamata ya kula da shi bayan an yi masa tiyata bai yi hakan ba. Bai gaya mana cewa sun dawo daga Sokoto ba. Akwai alluran da aka rubuta za a rika yi masa amma ba a yi ba."

Ya yaba wa likitocin da suka yi masa tiyata a Sokoto yana mai cewa da an bi ka'idojin da suka gindaya kunkurun ba zai mutu ba."Abin da muka yi masa shi ne mun hada wajen da zai iya haduwa da danyen bawon bayan nasa, sannan akwai inda ya tararratse da yawa da ba zai gyaru ba, sai muka samu wani abu muka rufe wajen, in ji Dr. Nura.

Ya kara da cewa tsawon wajen da ya fashe ya kai inci 12, fadinsa kuma ya kai inci bakwai.

Kwanson kunkurun yana ba shi kariya yana kuma yi masa amfani daidai da wajen da kunkurun ke rayuwa.

Post a Comment

0 Comments

Ads