Jerin manyan Malaman musulunci 5 da su ka yi Allah wadai da halin da ake ciki Na matsi A Nigeria

 Ana fama da matsanancin tsadar rayuwa a Najeriya a daidai wannan lokaci


Gwamnatin Tarayya ta yi sabon karin kudin shan wutar lantarki da man fetur


Malamai sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya duba halin da ake ciki


A cikin watan Satumban nan ne gwamnatin Najeriya ta yi sabon karin farashin man fetur, bayan haka kuma kudin shan wutar lantarki ya tashi a wurare da-dama.


Bugu da kari ana fama da matsanancin tashin kayan abinci da mutane su ka dogara da su. Wannan ya sa ta kai malamai, sun fara fitowa su na fadakar da hukuma.


Ga kadan daga cikin wadanda su ka yi magana game da halin da al’umma su ka shiga:


1. Ahmad Gumi


Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya tattauna da BBC Hausa a ranar Talata inda ya soki tsarin gwamnatin APC na rufe iyakokin kasa, ya ce wannan ya jawo mutane su ke fuskantar tsadar kayan abinci.


2. Lawal Shuaibu Abubakar


Lawal Shuaibu Abubakar wanda aka fi sani da ‘Malam Lawal Triumph’ a wani darasi ya roki gwamnatin tarayya ta saukaka talakawa a halin da ake ciki, malamin ya yi kuka da ya ke wannan jawabi.


3. Nasidi Goron-dutse


Sheikh Nasidi Abubakar Goron-dutse ya na cikin wadanda su ke wayyo Allah da yanayin da jama’a su ke ciki. Babban malamin ya ce tun da ya ke bai taba ganin al’umma su na wahala irin yanzu ba.


4. Bello Yabo


Sheikh Bello Yabo ya soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a dalilin tsadar kayan abinci da farashin man fetur. Yabo a wani karatu da ya ke yi, ya ce gwamnatin APC ta gaza, har gara mulkin baya.5. Sani Yahaya Jingir


Dattijon malamin nan na kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa duk da shekarunsa kusan 70 a Duniya, bai taba jin labarin irin tsadar da kayan abinci su ka yi a halin yanzu ba.

Post a Comment

0 Comments

Ads