Innalillahi Wani Likita Ya Gamu Da Ajalinsa A Hannun Barayin WayaWani bawan Allah likita dake aiki da Asibitin Aminu Kano, Atiku Tijjani Sha’aibu Rabo Ringim ya gamu da ajalisa bayan da Barayin waya suka kasheshi.

 


Sun kwace wayarsa ta karfin tsiya kamar yanda ‘yar uwarsa, Zainab Rabo Ringim wadda ke aiki da Radio Deutsche Welle ta tabbatar ta shafinta na Facebook.


Lamarin ya farune da misalin karfe 8 na dare a jiya, Alhamis, 10 ga watan Satumba, muna fatan Allah ya jikansa.

Post a Comment

0 Comments

Ads