Ina So A Rika Yanke Wa Masu Yin Fyade Hukuncin Kisa – Ministar Buhari


Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta yi kira da a rika zartar da hukuncin kisa kan miyagu masu aikata laifin fyade da sauran laifuka masu nasaba da cin zarafi.

Misis Tallen ta yi wannan kira ne yayin kaddamar da aikin iskar gas ta girki da kuma dashen itatuwa da aka gudanar ranar Juma’a a karamar Hukumar Girei ta jihar Adamawa.

Ministar ta kuma yi da’awar tsaurara hukuci a kan laifukan da suka shafi azabtar wa da sauran laifuka na cin zarafin kananan yara.

Tana cewa, “Karo na farko a tarihin Najeriya, mun samu shugaban kasar da bayar da muhimmanci a kan batutuwan da suka shafi cin zarafin mata da kananan yara.”

“Mata a Najeriya da kuma kananan yara su na ci gaba da jinjinawa shugaban kasar dangane da yadda ya dauki lamuransu da muhimmanci domin ci gaban kasa.”

“A saboda haka nake da’awar a rika yanke hukuncin kisa a kan wadanda aka kama da laifin fyade da kuma hukunci mai tsanani kan laifuka na cin zarafin kananan yara,” inji ministar.

Kiran ministar na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar fidiye masu fyade.
Aminiya Daily Trust

Post a Comment

0 Comments

Ads