HASASHE: ME ZAI FARU IDAN SHUGABA BUHARI YA KAMMALA WA'ADIN MULKINSA? NIGERIA

ME ZAI FARU IDAN SHUGABA BUHARI YA KAMMALA WA'ADIN MULKINSA?

DAGA Datti Assalafiy

Ba na so, kuma bana fatan bayan Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulki mutanen Arewacin Nigeria su zo suna cewa gara lokacin Buhari game da saukin rayuwa da tsaron rayukan su, hakan yana nuna mun ci baya, kuma mun 'kara shiga damuwa kenan a bayan Buhari


Ko kadan bana fatan haka ta faru gare mu, amma na fahimci mun dauko hanyar da nan gaba zamu zo muce gara mulkin Buharin akan duk wanda zai zo bayan sa daga kowace jam'iyya PDP ko APC.


Wallahi burina shine bayan shugaba Buhari ya sauka muzo muna cewa yanzu kam Alhamdulillah, a baya ansha wahala, amma yanzu kam rayuwa ta 'kara sauki ba kamar baya ba.


Sai dai na fahimci da wahala nan gaba mu fadi hakan, ba dan komai ba sai saboda wasu abubuwa guda uku:-

1. Na farko alakar mu da Allah, galibin mu bamu da wata kyakkyawar alaka tsakanin mu da Mahaliccin mu, banda sabon Allah da aikata miyagun zunubi babu abinda yake gudana a tsakanin mu, duk al'ummah musamman Musulma da ta rungumi wannan to ta shiryawa shan wahala da ganin fitina


2. Abu na biyu, harshen mu, da bakin mu bamu iya fadin alkhairi, mutanen da a baya ko Masallaci basa iya shiga hankali a kwance, saboda suna cikin tsoro da fargabar bomb zai kashe su suna sallah, yau sun manta da wannan babu wanda yake tunanin bomb zai kashe shi a masallaci.


Wadannan mutanen sune yau suke cewa gara Allah Ya mayar damu baya lokacin Jonathan, saboda tsaban rashin tunani da toshewar basira?


Mutanen da basu iya shiga kasuwa sai an caje su, basa iya shiga masallaci sai anyi bincike har cikin aljihu, tashar mota kana tsoro kana tunanin bomb zai tashi, balle masallacin Idi da ya zamo kasuwar sayar da rayuka da shahada da gonar gawarwakin 'dan-adam..

Mutanen da suka samu kan su a irin wancan mawuyacin halin, yanzu babu, sun manta sun koma butulci ma Allah suna cewa da tashin Dalar Amurka gara tashin bomb.

Suna izgili ma Allah suna cewa gara tashin Bomb da tashin farashin shinkafa, gara tashin bomb da tashin dala, Allah Ya zuba mana ido kawai yana kallon mu, mu saurari lokacin da zamu girbi sakamakon irin wadannan furucin saboda butulci ne wa ni'imar Allah, yau galibin mutane suna cewa gara wancan lokacin da yanzu? Subhanalllah😭

Allahu Akbar!

Mutane suna cikin wahalar rayuwa a yau, mutane suna cikin damuwa ta bangarori da dama, amma wallahi wannan bai kai muyi buri ko fatan Allah Ya mayar damu baya ba lokacin mulkin Goodluck Jonathan da Boko Haram suke

Post a Comment

0 Comments

Ads