'Yan Bindiga: An kashe mutum 1 da kuma sace mata da dama a wani sabon hari a Katsina

 ‘Yan Bindiga sun kashe wani Mutum, Ashiru Aliyu dan shekaru 50 a garin Daulai dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

 


Lamarin ya faru da safiyar jiya, Litinin, inda kuma ‘yan Bindigar suka sace mata da kayan Abinci da dabbobi a kauyen.


Wasu mazauna garin saidai guduwa suka yi kauyuka dake kusa dasu. ‘Yan Bindigar su kusan 30 su shiga garinne da Misalin karfe 1 na dare inda suka fara harbin Kan mai uwa da wabi.


Kakakin ‘yansandan jihar, SP Gambo Isa ya tabbatar da mutuwar Ashiru saidai bai bayar da bayani kan yawan matan da aka sace ba.

Post a Comment

0 Comments

Ads