(Bidiyo) Duk masu ihun 'Sai Baba' har yanzu munafukai ne, ko Buhari bai iya zuwa Katsina - Sheik Bello Sokoto

Wani shahrarren malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Sokoto, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan matsalar rashin tsaro da ya addabi Najeriya da kuma halin kunci da wuyan da gwamnatinsa ta jefa yan Najeriya.Sheikh Sokoto a faifan bidiyo da jaridar SaharaReporters ta gani yana mai cewa yan bindiga suna cin karansu ba babbaka a garuruwa.


Ya ce idan Buhari ya ki kawo sauyi da gyara, shi da al'ummarsa za suyi addu'a Allah ya kawar da shi.


Shehin Malamin ya caccaki masu yabon Buhari har yanzu inda yace munafukai ne saboda ku shi Buharin ya kasa zuwa mahaifarsa jihar Katsina sakamakon rashin tsaro.Yace: "Za mu cigaba da magana kan Zakkah, amma akwai bukatar in yi muku jawabi kan halin kuncin da kasarmu ke ciki yanzu. Wannan tsohon (Buhari) ya kaimu bango."


"Gaskiyar magana itace, talauci da kunci da muke fuskanta yanzu gwamnatin tarayya ce ta haddasa. Muna samun abinci ta iyakoki amma saboda muguntan Buhari ya kullesu."


"Duk masu cewa 'Sai Baba' 'Sai Baba' makaryata ne, munafukai ne marasa amfani. Ko mutumin da suke yiwa ihu 'Sai Baba' ba zai iya zuwa Katsina ba yanzu. Ya san irin haushin da mutane zasu fuskanceshi da shi."


"Muna addu'a Allah ya shiryi Janar Buhari yayi gyara, yayi ayyukan kwarai matsayin shugaba, amma idan ya cigaba a haka, muna addu'a Allah ya mayeshi da mafificin shugaban."


A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta siffanta sukan da jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takarar shugaban kasarta a zaben 2019, Atiku Abubakar, kan tashin kudin man fetur a matsayin kololuwar munafinci.


Jam'iyyar ta kara da cewa babatun da Atiku ke yi ya nuna cewa munafiki ne kuma ya bayyana shi matsayin "mutum mara gaskiya kuma wanda bai cancanci a taba yarda da shi ba."


Mataimakin kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba.

Post a Comment

0 Comments

Ads