Babu Abunda Na Amfana Da Shi Banda Tashin Hankali Da Tashin Kayan Abinci

BABU ABUNDA NA AMFANA DA SHI BANDA TASHIN HANKALI DA TASHIN KAYAN ABINCI GASHI ANA TA KASHE MANA YAN'UWA A GARIN MU


Hoton wanda aka dauke shi gabanin zabukan shekarar 2015 a Jihar Kaduna, an dauki bawan Allan ne mai lalurar nakasa mai suna Abdullahi Aliyu, a lokacin da yake kokarin baiwa Shugaban kasa Muhammad Buhari, da Jam'iyyar sa ta APC tallafi don kafa Gwamnati, a yan kwanakin nan ana ta yawo da hoton mutumin a sabbin kafafen sadarwa inda al'umma da dama suka dunga bayyana raayoyi game da mutumin har ana cewa ya sha Jar-Miya,a saboda haka ne wakilin mu Shuaibu Abdullahi, yayi tattaki don jin shin kwalliya ta biya kudin Sabulu?

To sai dai Malam Abdullahi Aliyu, mazaunin Jihar Kaduna, ya ce babu wani abun daya amfana da shi a Gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari, banda tashin hankali, tsadar kayayyakin abinci, gashi ana ta kashe mana Yan'uwa a garin can Jihar Zamfara.

To bazan ce kwalliya bata biya kudin Sabulu ba tunda ni dan Allah na baiwa Buhari tallafi, kuma Najeriya da sauran Al'umma su sami ci gaba idan aka kafa sabuwar Gwamnati,sai dai ba yadda aka zata ba, ana fama da kashe-kashe a sassan Najeriya;inji shi

Malam Abdullahi Aliyu, ya kara da cewar labari ya karade gari cewar an bani manyan kudade, wallahi ni babu wanda ya temake ni banga kowa ba kuma babu wanda ya aiko mun da sako.

Wallahi ina neman temako Maganar da ake yi ko matsugunni bani da shi rayuwa ta mun wuya, babu wanda ya taba temaka mun tunda aka kafa sabuwar Gwamnati, Dan Allah Dan Annabi a temake ni.

Post a Comment

0 Comments

Ads