Babbar Magana! Yadda Dan Sanda Ya Saci Kudi Har 280,000 A Cikin Gida Daga Zuwa Kama Wani

 

Babbar Magana Wani mai aski, Atighan Sam ya zargi jami'in dansanda da shiga gidansa ya lalata masa kayan amfani da kuma sace masa kudi 280,000.   Lamarin ya farune a Diobu dake birnin Fatkwal ta jihar Rivers da misalin karfe 12 na daren Juma'ar data gabata. 

 

Sam yace yaji dansandan na tambayar makwabta cewa a nuna masa gidansa dan hakane ya samu ya tsere kamin ya sameshi a ciki.   


Yace dansandan ya shigar masa gidane bisa rakiyar wasu abokan aikinsa 2 inda yayi zargin ya kai masa harinne saboda yaki biya masa kudin giyar da ya sha shi da wasu abokansa a wata mashaya.   


Me Askin ya bayyana cewa ya kaiwa 'yansanda korafi kan lamarin inda kuma an gayyaci dansandan da ake zargi me suna Usman dan yin bincike.

Post a Comment

0 Comments

Ads