Ba Zan Sake Yi Wa Buhari Waka Ba Sai Talawa Sun Hada Dubu-Dubu Sun Dauki Nauyin Wakar -Rarara

 Dauda Kahutu Rarara Shaharerren mawakin 'yan siyasar Najeriya musamman shugan kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyan APC Aminiya


Fitaccen mawakin 'yan siyasar nan da masu mulki a Najeriya wato Dauda Kahutu Rarara, yace daga yanzu ya daina yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari waka, har sai masoyan shugaban kasar sun biyashi kudin rera wakar


A zantawar sa da wakilin RFI Hausa Abuabakar Isah Dandago, Rarara, yace irin cece kucen da ya karade kafafen sada zumunta kan cewar shugaba Buharin ya gaza ya sanya shi soma shelar neman masoyan shugaban na zahiri da suka kada masa kuri’a su yi karo karon naira dubu guda guda matsawar sunason ya dawo fagen cigaba da yiwa Buharin waka, idan kuwa bahaka ba shikam bazai kara yiwa shugaban waka ba.


Rarara wanda ya yi suna wajen yada manufar shugaban Najeriyar ta hanyar wakokin sa, yace a tasa fahimtar wadanda ke sukar shugaba Buhari ba sune suka kada masa kuri’a ba, illa dai masu neman dakushe masa farin jini.

Inji mawakin duk da yadda ake ganin al’amura sun rinchabe a Najeriyar, shugaba Buhari ya yi rawar gani a bangarori da dama.


Kuna iya sauraren cikakkiyar hirar sa da gidan redion a cikin wannan video dake kasa
Post a Comment

0 Comments

Ads