Asiri Ya Tonu! An Cafke Wata Mata Data Guntule Hannunta Da Gangan Dan Kawai A Biyata Diyya

Mahukuntan a kasar Slovenia sun kama wata mata, da ake zargin ta guntule hannunta dan kawai a biyata wata Inshora me tsoka.
Matar me shekaru 21 da taimakon ‘yan uwanta ta guntule hannun nata da Zarto inda aka garzaya da ita Asibiti, kamar yanda Mahukuntan suka bayyana saidai ‘yan uwan nata basu je da Hannu  da aka guntule zuwa Asibitin ba inda suka yi ikirarin ta tankene yayin da take yankan Bishiya.
Da bincike yayi zurfi an gano guntulallen hannun matar a gidansu kuma tuni aka kamata tare da wasu ‘yan uwanta 2 da ake zargi da wannan aika-aika.

Post a Comment

0 Comments

Ads